ABNA24 : A cikin wani bayani da kungiyar ta fitar, ta sanar da cewa wani jirgin leken asirin Isra’ila ya shigo cikin kasar Lebanaon daga iyakokin kudancin kasar, kuma tuni mayakan kungiyar suka harbor shi.
Bayanin ya ce jirgin leken asirin na Isra’ila ya keta hurumin sararin samaniyar kasar Lebanon, a kan hakan dakarun kungiyar ba su bata lokaci ba wajen harbor kasa.
Wasu daga cikin kafofin yada labaran Isra’ila sun bayar da rahoton bacewar jirgin leken asirin Isra’ila a cikin kasar Lebanon, kamar yadda kakakin rundunar sojin yahudawan Isra’ila ma ya tabbatar da hakan, inda ya ce jirgin ya fadi a kudancin kasar Lebanon.
Kungiyar Hizbullah dai ta sha nanata cewa, lokaci ya wuce da Isra’ila za ta rika cin karenta babu babbaka a cikin kasar Lebanon, inda a halin yanzu tana da kyakkyawan shiri na tunkarar irin wadannan ayyuka na tsokana da Isra’ila take yi a kan kasar Lebanon, daga ciki kuwa har da kakkabo irin wadannan jirage na leken asiri.
Hakan kuma kungiyar ta tabbara da cewa za ta iya mayar da mummunan martani a cikin Isra’ila da makamai masu linzami, matukar dai ta yi gigin sake kaddamar da wani hari a kan kasar ta Lebanon a halin yanzu.
342/